Boko Haram sun kashe sojoji 11 a Kaduna

74

Mayakan Boko Haram sun kai hari kan wani sansanin soji a yankin Falwaya dake Birnin Gwari a jihar Kaduna, inda suka kashe sojoji 11 tare da raunata wasu 19.

Wasu ‘yan kato da gora uku suma sun rasa rayukansu, yayin da wasu biyu suka ramu raunuka a lokacin harin.

An rawaito cewa yayin fadan na awanni 3 da rabi, wanda aka fara da misalin karfe 4 da rabi na yamma, aka gama da misalin karfe 8 na dare, an kone wasu manyan bindigogin yaki guda 3, bayan an raba sojojin da sansaninsu.

Majiyoyin tsaro sunce wajen da aka kai harin babbar hanya ce da ‘yan ta’adda ke tsallakawa daga jihar Neja zuwa jihar Zamfara.

An bayar da rahoton cewa kayayyakin yakin da aka yi asara sun hada da kananan bindigogi; da babbar bindiga da bindigogi 14 samfurin AK47 da babura 10, da sauransu.

Duk da kasancewar an kara turo da wasu sojoji daga sansanin Gwaska da misalin karfe 9 da kwata na dare, babu tabbacin adadin wadanda aka kashe daga bangaren Boko Haram.

A wani labarin kuma, babban hafsan sojin kasa, Faruk Yahaya, ya nanata jajircewar sojin Najeriya wajen dakile dukkan nau’in rashin tsaro dake addabar kasarnan.

Faruk Yahaya ya bayar da tabbacin a yau yayin wani taron wuni guda da sashen kirkire-kirkire na helkwatar sojoji ya shirya a Abuja.

Babban hafsan sojin kasan, wanda ya samu wakilcin shugaban sashen kudiri da tsare-tsare na sojoji, Anthony Omozoje, yace matsaloli da kalubalen tsaro dake fuskantar kasarnan ya haifar na bukatar sake duban tsarin tsaron kasarnan domin magancewa.

Yace duk da kalubalen tayar da kayar baya da ta’addanci da garkuwa da mutane da fashin daji da sauransu, kungiyoyin ‘yan ta’adda na cigaba da haifar da barazana ga zaman lafiyar kasarnan.

Faruk Yahaya yace sojojin suna cigaba da mayar da martani babu kakkautawa da nufin magance dukkan wani kalubale bisa turbar jawabinsa na kama aiki, wanda yayi alkawarin dakile dukkanin kalubalen tsaron kasarnan.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

eight + two =