Shugabannin kasashen yammacin Afirka na kungiyar ECOWAS sun yanke shawarar tura dakaru zuwa kasar Guinea Bissau domin taimakawa wajen daidaita al’amura a kasar bayan yunkurin juyin mulkin da bai kai ga nasara ba.
Sai dai kungiyar ba ta bayyana adadin dakarun da za ta aika da kuma lokacin da za a tura su ba.
A cikin wata sanarwa da ta fitar bayan taronta a Accra, babban birnin kasar Ghana, kungiyar ECOWAS ta ce ta yanke shawarar kin sanya wa Burkina Faso karin takunkumi bayan juyin mulkin da aka yi a kasar a watan jiya.
A wani labarin kuma, mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya ce shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS sun sake jaddada matsayarsu na cewa kwata-kwata babu wani uzuri na sauya gwamnati ta hanyar juyin mulki.
Ya bayyana hakan ne a jiya bayan halartar babban taron kungiyar ECOWAS da aka gudanar a Accra, babban birnin kasar Ghana, kuma tattaunawar da aka yi a taron ta shafi harkokin siyasa a kasashen Burkina Faso, Mali da Guinea.
Mataimakin shugaban kasar ya ce a ra’ayin kungiyar ECOWAS, hanya daya tilo ta sauya gwamnati a yankin da aka amince da ita, ita ce ta hanyar demokradiyya.
Farfesa Osinbajo wanda ya wakilci shugaban kasa Muhammadu Buhari a wajen taron, ya amsa tambayoyi daga manema labarai kan sakamakon taron.
A wata sanarwa da kakakinsa Laolu Akande ya fitar, ya ce mataimakin shugaban kasar ya dawo Abuja da yammacin jiya daga birnin Accra.