Kwamishinan ilimi, kimiyya da fasaha na jihar Jigawa, Dakta Lawan Yunusa Danzomo ya kaddamar da kwamitin kwararru domin sake duba yawan shekarun ritaya na malaman makaranta.
A jawabin da ya gabatar lokacin kaddamar da kwamatin, Lawan Danzomo ya ce bisa la’akari da irin mutanen da aka zabo, akwai tsammanin cewa wakilan kwamatin za su fito da shawarwari irin na kwararru domin aiwatar da tsarin yadda ya kamata.
Ya ce kwamatin zai tantance tare da gano kwararrun malamai da suke da takardun kwarewar aikin koyarwa, kuma suke aiki a matsayin malamai ko jami’an gudanar da mulki a bangaren ilimi.
A nasa jawabin, a madadin wakilan kwamatin, babban sakataren sashin bunkasa kwazon ma’aikata da bayar da horo, Ahmed Rufa’i Datti, ya godewa gwamnatin jiha bisa basu wannan dama, tare da alkawarin sauke nauyin da aka dora musu.
Kwamatin da aka bawa wa’adin makonni uku ya gabatar da rahotonsa, yana da babbar sakatariyar ma’aikatar ilimi Hajiya Safiya Muhammad a matsayin shugaba, yayin da daraktan sashin ayyuka na musamman na ma’aikatar, Kamilu Ibrahim, zai yi aiki a matsayin sakatare.