Gwamnati ta rufe titunan zuwa sakateriyar tarayya

6

Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin rufe titunan zuwa gine-ginen sakateriyar gwamnatin tarayya da ma’aikatar harkokin kasashen waje dake Abuja.

Shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya, Dr Folasade Yemi Esan, ita ta bayar da umarnin cikin wata sanarwar da daraktan sadarwa a ofishin shugabar ma’aikata, Abdulganiyu Aminu, ya fitar a Abuja.

Yemi-Esan tace za a rufe titunan bisa la’akari da bikin tunawa da mazan jiya na bana, wanda ake yi domin karrama sojojin da suka rasu a bakin aiki.

Tace bikin wanda za gudanar a gobe zai samu halartar shugaban kasa Muhammadu Buhari da sauran manyan jami’an gwamnati.

Ana gudanar da bikin tunawa da mazan jiya a ranar 15 ga watan Janairun kowace shekara domin karrama sojojin da suka mutu a guraren yaki daban-daban da wajen ayyukan kasa.

A wani cigaban mai alaka da wannan, gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje a jiya ya kaddamar da asusun tallafawa sojoji domin ranar tunawa da mazan jiya, inda ya bayar da gudunmawar naira miliyan 2.

A wani taro da aka gudanar a gidan gwamnatin Kano domin tunawa da mazan jiyan tare da tara kudaden tallafawa tsofin sojojin, gwamnan wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Nasir Yusuf Gawuna, ya kuma sanar da gudunmawar naira miliyan 1 daga kwamishinoninsa da naira miliyan 4 da dubu 400 daga kananan Hukumomi 44, yayin da babban mai kaddamarwa, Abdussalam Zaura ya bayar da gudunmawar naira miliyan 2.

A jawabinsa, gwamnan yace manufar bikin ita ce karramawa da jinjina sadaukar da kan sojojin da suka mutu da kuma tunawa da dukkan wadanda ke aikin tsaron kasarnan, musamman a yaki da ta’addanci, garkuwa da mutane, da fashin daji a kasarnan.

A nasa jawabin, shugaban kungiyar tsaffin sojoji ta kasa, reshen jihar Kano, Abdullahi Bagobiri, ya godewa gwamna Ganduje bisa goyon baya da kulawar da yake bawa tsaffin sojoji tare da iyalansu.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

five × three =