Buhari ya kaddamar da ayyukan bayan harin Boko Haram a Maiduguri

92

Akalla mutane 5 aka tabbatar da mutuwarsu bayan wasu bama-bamai sun fada a kusa da filin jirgin saman Maiduguri kimanin sa’a daya kafin isowar shugaban kasa Muhammadu Buhari jihar Borno a wata ziyarar aiki.

Bama-baman da ake kyautata zaton an harba su ne daga wajen birnin sun fara sauka a wurare daban-daban a kusa da filin jirgin da misalin karfe 10 da mituna 45 na safe.

Shaidu da majiyoyin tsaro da ke da masaniya kan lamarin sun tabbatar da cewa akalla wasu bama-bamai guda biyar ne suka fado a galibin wuraren da jama’a ke zaune, lamarin da ya yi sanadiyar asarar rayuka da jikkata fararen hula da dama.

Wata majiya da ta zanta da manema labarai ta ce daya daga cikin bama-baman ya fado ne a unguwar Ayafe da ke wajen Ngomari, inda ya kashe mutane hudu ciki har da wata budurwa ‘yar shekara 16.

Wasu bama-bamai sun fada a Ajilari Cross, Moromti da kuma rukunin gidajen Legacy da ke Bulumkutu.

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da ayyuka a Maiduguri a ziyarar aiki ta yini daya da ya kai jihar Borno.

Kamfanin Dillancin Labarai na kasa ya bayar da rahoton cewa, a yau jirgin shugaban kasar ya sauka a sashin rundunar sojojin saman Najeriya na filin jirgin saman Maiduguri da misalin karfe 12 saura kwata na safe.

Shugaban kasar ya samu tarbar Gwamna Babagana Zulum da mataimakinsa Usman Kadafur da ‘yan majalisun tarayya da na jiha da wasu manyan jami’an gwamnati.

Sauran jiga-jigan da suka tarbi shugaban kasar sun hada da babban hafsan soji, Farouq Yahaya da kwamandan Operation Lafiya Dole, Christopher Musa, shugabannin hukumomin tsaro, al’umma da malaman addini.

A yayin ziyarar tasa, shugaban kasa ya kaddamar da cibiyar karatu daga gida ta Muhammadu Indimi da cibiyar taro ta kasa da kasa, wadanda dukkansu aka gina a jami’ar Maiduguri.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

2 × three =