Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa rashin tsaro a yankin Arewa maso Yamma ya tilastawa sama da mutane dubu 11,500 tserewa zuwa makwabciyar kasar Nijar cikin watan Nuwamba.
Kakakin hukumar Boris Cheshirkov ne ya bayyana hakan a yau a wani taron manema labarai a birnin Geneva na kasar Switzerland.
Ya ce akasarin wadanda suka gudu Nijar cikin watan Nuwamba sun sami mafaka a kauyuka 26 da ke fadin Bangui a yankin Tahoua na jamhuriyar Nijar wanda tuni yake da ‘yan gudun hijirar Najeriya 3,500 tun watan daga watan Satumba.
Ya kara da cewa mata da kananan yara ne suka fi yawa daga cikin wadanda suka shiga Nijar kwanannan.
Ya bayyana cewa rikicin ya biyo bayan rikicin kabilanci tsakanin manoma da makiyaya.
Hukumar ta yabawa Nijar a matsayin abar misali na hadin kai da karamci a yankin da ke fama da rikice-rikice.