Gwamnatin tarayya ta bukaci ‘yan jarida su shiga shirin yakin da maleriya

12

Gwamnatin tarayya ta ce kafafen yada labarai a Najeriya ba sa bayar da rahotannin zazzabin cizon sauro duk da cewa an gano cewa na daya daga cikin matsalolin da suka shafi kiwon lafiya a kasar inda aka kiyasta yana jawo kashi 30 cikin 100 na mutuwar yara da kuma kashi 11 cikin dari na mace-macen mata masu juna biyu a duk shekara.

Hakan ya fito ne a cewar shugabar yaki da cutar zazzabin cizon sauro na kasa, Beeve Hua a taron wayar da kan manema labarai kan rabon gidajen sauro da aka gudanar a harabar ma’aikatar lafiya ta jihar Jigawa dake Dutse.

Ya ce zazzabin cizon sauro ya kasance matsala ce da ta fi zama ruwan dare kuma wadda za a iya magance ta a Najeriya duk da haka tana kashe kashi 97 cikin 100 na ‘yan Najeriya musamman yara ‘yan kasa da shekara biyar da mata masu juna biyu.

Beeve ya bayyana cewa, bisa ga binciken da aka yi dangane da zazzabin cizon sauro, Najeriya na da kusan mutane miliyan 110 da ke kamuwa da cutar a duk shekara.

Ya ce barazanar ta haifar da wani gagarumin nauyi na zamantakewa da tattalin arziki a kasarnan, kuma ana asarar biliyoyin Nairori a duk shekara ta hanyar kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro ta tsadar maganin cutar.

A wani labarin kuma, Gwamnatin tarayya ta kalubalanci matasa da su yi amfani da fasahar kere-kere wajen koyon sabbin sana’o’i, da zama ‘yan kasuwa da kuma samar da sabbin ayyukan yi.

Babban mataimakiya na musamman kan dabarun sadarwa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, Misis Oge Funlola Modie, ita ce ta bayar da wannan umarni yayin taron horas da matasa da gidauniyar Barista Sam Otoboeze ta gudanar a Abuja.

Ta kuma ce akwai bukatar a tallafawa matasa domin cimma burinsu.

Ta ce horon wata dama ce ta koyo, zama dan kasuwa da samar da sabbin ayyukan yi.

Sam Otoboeze, wanda shi ne ya kafa gidauniyar, ya ce dole ne a yi amfani da matasa miliyan 55 da ba su da aikin yi a Najeriya, domin kawo karshen rashin tsaro a Najeriya.

An gudanar da shirin ne tare da hadin gwiwar gidauniyar Ochima Foundation.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

twelve − 2 =