Gwamnatin Borno ta sake bude titin Bama-Banki

18

Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya sake bude hanyar Bama zuwa Banki mai tsawon kilomita 76 domin dawo da harkokin kasuwanci tsakanin Najeriya da kasashen Kamaru da Chadi da ke makwabtaka da Najeriya.

An rufe hanyar ne a shekarar 2012, saboda ayyukan mayakan Boko Haram.

Da yake jawabi a wajen bikin bude hanyar, jiya a Bama, Gwamna Zulum ya ce ba za a samu wani cigaba mai ma’ana ba a yankunan da aka kwato, har sai an dawo da harkokin kasuwanci.

Ya kuma yabawa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa jajircewarta na maido da zaman lafiya a jihar Borno.

Gwamnan ya bayyana cewa kokarin da sojoji suka yi a jihar ya sa aka fadada ayyukan noma a bana musamman a yankunan da a baya basa shiguwa.

A jawabinsa na maraba shugaban karamar hukumar Bama, Aji-Kolo Kachalla, ya yaba da wannan cigaban, inda ya bayyana hakan a matsayin wani babban taimako ga al’ummar yankin da suka shahara wajen kasuwanci.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

1 × five =