Kudin internet na babban bankin kasa (CBN) mai suna eNaira ya fara aiki bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da shi yau a hukumance.
An kaddamar da kudin a fadar shugaban kasa dake Abuja. A baya an dage shirin kaddamar da kudin na internet a ranar 1 ga watan Oktoba.
Najeriya daya ce daga cikin kasashe kalilan a duniya wadanda suka kirkiri kudin internet.
Wani kamfanin Bitt ne ya samar da eNaira, kamfanin kuma shine wanda ya samar da kudaden internet na wasu kasashen nahiyar kudancin Amurka.
A wajen bikin kaddamarwar a yau, gwamnan babban bankin kasa (CBN), Godwin Emefiele, yace tuni aka samar da kudin eNaira miliyan 500.
Tuni aka fara sauko da manhajojin asusun kudin na internet a wayoyin android da iphone.
Wani bayani a shafin internet na eNaira ya bayyana yadda kudin da asusunsa za suyi aiki.