Gwamnatin Tarayya ta ware N600bn domin ba wa manoma bashi

39

Gwamnatin Tarayya a karkashin shirin inganta rayuwa da habaka aikin gona ta ware kudi naira miliyan dubu 600 da za ta bayar a matsayin bashi domin tallafawa manoma miliyan 2 da dubu 400 a fadin kasarnan.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sanar da haka jiya a Abuja a wajen bikin bude baje kolin kayan aikin gona na kasa domin ranar abinci ta duniya ta bana.

Shugaba Buhari, wanda ya samu wakilcin ministan aikon gona da raya karkara, Mohammed Abubakar, yace za a bayar da bashin ba tare da kudin ruwa ba.

A nasa bangaren, shugaban kwamitin aikin gona na majalisar dattawa, Sanata Abdullahi Adamu, yace gwamnatin Shugaba Buhari ta kirkiri shirye-shirye da kudirori akan cigaban aikin gona da yalwar abinci a kasarnan.

A wani labarin kuma, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a jiya ya nemi agajin shirin cigaba na majalisar dinkin duniya wajen sake tsugunnar da ‘yan gudun hijira a Arewa maso Gabas.

Yayi magana a fadar shugaban kasa da ke Abuja lokacin da ya karbi bakuncin shugabar shirin cigaba na majalisar dinkin duniya, shiyyar Afirka, Ahunna Eziakonwa.

Shugaba Buhari yace shirin cigaba na majalisar dinkin duniya ya cancanci yabo saboda tallafin da ya bawa Najeriya zuwa yanzu, a bangarori daban-daban, musamman wajen samar da zaman lafiya a Arewa maso Gabas.

Yace gwamnati na yin iya bakin kokarinta wajen sake tsugunnar da ‘yan gudun hijira a gidajensu, amma yayi nuni da cewa da kudade kalilan, kuma za ayi maraba da tallafin hukumomi irinsu shirin zaman lafiya na majalisar dinkin duniya.

Ya godewa Ahunna Eziakonwa wacce ‘yar Najeriya ce bisa ziyarar da ta kawo, inda yayi nuni da cewa da ita da Ngozi Okonjo-Iweala ta hukumar cinikayya ta duniya da Amina Mohammed, mataimakiyar sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya, suna fitar da Najeriya kunya a idon duniya.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

two × five =