A koma gona domin magance kalubalen tattalin arziki – Buhari

29

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari cikin wata tattaunawa da aka watsa a jiya yayi watsi da alkaluman tabarbarewar tattalin arziki a karkashin mulkinsa inda yake kira ga ‘yan Najeriya su rungumi aikin gona domin magance tulin matsalolin tattalin arzikin kasarnan.

A tattaunawar, wacce ma’aikatan gidan talabijin na Channels, Seun Okinbaloye da Maupe Ogun-Yusuf suka gabatar, shugaban kasar ya musanta wasu daga cikin alkaluman da masu gabatarwar suka lissafa dake nuna tattalin arzikin Najeriya ya tabarbare tun bayan hawansa mulki a shekarar 2015.

A tattaunawar, Okinbaloye ya kwatanta alkaluman tattalin arziki tsakanin shekarun 2015 da 2021, inda yayi bayanin yadda alkaluman suka damu ‘yan Najeriya dangane da mummunan halin matsin tattalin arziki.

Amma shugaba Buhari ya mayar da martani ta hanyar watsi da alkaluman da ‘yan jaridar suka lissafa, sai dai ya kasa kare kansa. Daga baya ya sake maimata ikirarinsa na cewa dole ‘yan Najeriya su koma gona kafin a iya gyara tattalin arziki.

Shugaban kasar yayi ikirarin cewa kashi 2 da rabi cikin 100 ne kadai na kasar noma a kasarnan ake iya nomawa.

A wani batun kuma, shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Iyorchia Ayu, yace dabara ta karewa shugaban kasa Muhammadu Buhari akan yadda zai ciyar da kasarnan gaba.

Iyorchia Ayu ya fadi haka a matsayin martani akan matsayar shugaban kasa kan wasu batutuwa a tattaunawarsa da gidan talabijin na Channles a jiya.

Daga cikin batutuwan da shugaba Buhari yayi magana akai sun hada da rikicin makiyaya da manoma da neman kirkirar yansandan jihoshi da takaddamar dokar zaben da aka gyara da kalubalen tsaro da kuma zaben shugaban kasa na shekarar 2023.

Da yake mayar da martani akan sabunta matsayar shugaba Buhari akan rikicin makiyaya da manoma, Iyorchia Ayu ya zargi shugaban kasar da nuna halin ko in kula akan zubar da jinin da kudirin ke haifarwa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

5 × 1 =