Buhari ya amince kwangiloli 878 daga 2015 zuwa yanzu

27

Majalisar zartarwa ta tarayya ta bayar da kwangiloli 878 a jumlace tun farkon gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari daga watan Mayun 2015 zuwa yanzu.

Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha ne ya bayyana hakan a jiya yayin bude wani taron bita na kwanaki biyu na ayyukan ministoci a Abuja.

Sai dai, bai bayar da cikakkun bayanai game da kwangilolin ba amma yace an amince da su ne don samar da ababen more rayuwa, wanda aka tsara don bayar da damar habaka tattalin arziki da samun cigaba cikin gaggawa.

An shirya taron ne domin tantance cigaban da aka samu wajen cimma muhimman abubuwa guda 9 na gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnati da suka hada da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo da Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan da Kakakin Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila.

A wani cigaban mai alaka da wannan, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya ce akalla manoma miliyan 6 da dubu 390 aka zaba daga jihoshi domin cin gajiyar shirin dorewar tattalin arziki, na bangaren aikin gona.

Yemi Osinbajo ya bayyana hakan ne yayin gabatar da shirin a lokacin bikin bude wani taron bita na kwanaki biyu na ayyukan ministoci a jiya a dakin taro na fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a bara ya umarci Osinbajo, wanda yake jagorantar kwamitin dindindin na tattalin arziki, da ya jagoranci aiwatar da shirin dorewar tattalin arzikin na naira tiriliyan 2 da biliyan 300 da nufin rage illar cutar corona ga tattalin arziki.

Mataimakin shugaban kasar ya ce an tabbatar da manoman da aka zaba tare da gonakinsu inda za su samu tallafin.

Ya ce an share kadada 320 na gonaki a wasu jihoshi, inda aka samar da kadada 40 a kowace jiha.

Osinbajo ya lissafa jihohin da suka hada da Kwara da Filato da Cross River da Edo da Kaduna da Ekiti da kuma Osun.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

eleven − 6 =