Buhari ya lashe lambar yabo ta duniya kan gaskiya da yaki da cin hanci da rashawa

39

An karrama shugaban kasa Muhammadu Buhari da lambar yabon gwarzon yaki da cin hanci da rashawa daga cibiyar kwararrun masu binciken almundahana ta kasa.

An karrama shugaban kasan da lambar yabon bisa la’akari da sadaukarwar da ya yi a tsawon rayuwarsa wajen yaki da cin hanci da rashawa da sadaukar da kai tare da gaskiya.

Shugaban kwamitin gudanarwa na kwamitin amintattu na cibiyar, Dr Iliyasu Gashinbaki ne ya bai wa shugaban kasa lambar yabon jiya a Abuja.

Lambar yabon dai ita ce babbar lambar yabo mafi girman ta cibiyar da aka kebe ga shugabannin kasashen Afirka kadai, wadanda ke da halaye nagartattu da dabi’u masu kyau.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari shine shugaban Afrika na farko da aka baiwa kyautar.

Da yake karbar kyautar, shugaba Buhari ya godewa cibiyar bisa karrama shi.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

4 × 2 =