Gwamnatin Zamfara ta ce an kama masu yiwa ‘yan bindiga leken asiri 2,000

327

Gwamnatin jihar Zamfara ta ce an kama sama da mutane dubu 2 da ake zargi da yiwa ‘yan fashin daji leken asiri, tun daga lokacin da ta katse hanyoyin sadarwa da fara kai farmakin sojoji a jihar.

Kwamishinan Yada Labarai na jihar, Ibrahim Dosara ne ya bayyana hakan a yau yayin wani taro da manema labarai a Kaduna.

Ibrahim Dosara ya ce wadanda aka kama, sun bayar da muhimman bayanai kan ayyukansu da kuma yadda ake zargin wasu manyan mutane ne suke daukar nauyinsu.

Ya ce an samu nasarar ayyukan tsaro a jihar, inda ya kara da cewa ‘yan bindiga da yawa sun tsere daga jihar kuma sauran na fama da yunwar da ta tilasta musu cin danyen abinci sakamakon takunkumin da gwamnati ta kakaba musu.

A wani labarin kuma, wani mashahurin jagoran yan fashin daji mai suna Muhammad Bello, wanda aka fi sani da Turji, ya mayar da helkwatasa daga Fakai a karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara, zuwa gabashin karamar hukumar Isa ta jihar Sokoto.

Wasu majiyoyi wadanda suka zanta da Premium Times sun ce mai yiwuwa Turji ya gujewa hare-haren da sojoji ke shirin kaddamarwa bisa umarnin gwamnatin jihar Zamfara.

Matashin mai shekaru 27 dan fashi ne mara tausayi da ke aiki a jihoshin Sokoto da Zamfara. A lokuta da dama, ya ki amincewa da yarjejeniyar zaman lafiya daga gwamnatocin jihoshi.

Lokaci guda da ya ce yana da bukatar tattaunawa shine lokacin da malamin addinin musulunci jihar mazaunin Kaduna, Sheikh Ahmed Gumi, ya ziyarci sansaninsa da ke Zurmi a Jihar Zamfara.

Turji ya kasance yana rike da mahaifi da kaka da kawun kakakin majalisar dokokin jihar, Nasir Magarya, wanda ya yi garkuwa da su tare da wasu mutanen, kimanin watanni biyu da suka gabata.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

four × four =