Buhari ya sauke Basheer Lado

53

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sauke Basheer Mohammed daga mukaminsa na Darakta Janar na hukumar hana safarar mutane ta kasa (NAPTIP).

An sallami Bashir Mohammed kasa da watanni hudu bayan ya karbi shugabancin hukumar.

Cikin wata sanarwa a yau, hadimin shugaban kasa kan yada labarai, Garba Shehu, yace shugaban kasar ya amince da nadin Fatima Waziri Azi a matsayin wacce zata maye gurbin Basheer Mohammed.

Garba Shehu nadin nata ya biyo bayan shawarar ministar jin kai, kula da annoba da walwalar jama’a, Sadiya Umar Faruk.

A ranar 27 ga watan Mayun bana, Basheer Mohammed yayi musayar mukaminsa na kwamishinan tarayya a hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta kasa tare da tsohuwar Darakta Janar ta hukumar hana safarar mutane ta kasa, Imaan Suleiman Ibrahim.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

eighteen − 6 =