Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da wani shiri da aka tsara don samar da sabbin damarmaki ga sabbin wadanda suka kammala karatu su dubu 20 a kowace shekara.
Da yake jawabi yayin bikin kaddamarwar a fadar shugaban kasa dake Abuja, Shugaba Buhari ya bayar da tabbacin cewa za a bayar da dama ga masu horo wadanda tuni ake basu horo a masana’antu daban-daban, kuma sun samu gogewar da ake bukata da iya aiki a cikin shekaru, don bayar da jagoranci da tallafi ga matasa ‘yan Najeriya.
A cewarsa, shirin zai samar da wata hanya ga matasan Najeriya don samun kwarewar aiki a manyan kamfanoni da samun dabarun da suka dace da gina ingantattun hanyoyin sadarwa na gaba a fannoni daban-daban da suka hada da fasahar sadarwa, da ayyukan kudi da kasuwanci, masana’antu, noma da aikin gona.
Sauran fannonin sun hada da hakar ma’adanai, sadarwar wayar salula, masana’antun fasaha, ilimi, lafiya, bincike da cigaba, da hukumomin gwamnati.