Gwamnati za ta bayar da bashi marar kudin ruwa ga ‘yan Najeriya dubu 98

46

Gwamnatin tarayya ta ce ta kammala shirin bayar da bashi marar ruwa ga mutane dubu 98 da suka cikin shirin koyar da sana’o’i da bayar da jari na gwamnatin tarayya a fadin kasar nan.

Ministar harkokin jin kai, kula da annboba da ci gaban jama’a, Sadiya Umar-Farouq, ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da mai taimaka mata na musamman kan harkokin yada labarai, Nneka Anibeze, ta fitar yau a Abuja.

Sadiya Umar-Farouq ta ce an cimma wannan matsayar ne bayan kammala tantance mutanen a kashin farko, wadanda suka cancanta kuma aka zabo su don cin gajiyar kananan basussuka da suka kama daga naira dubu 50 zuwa naira dubu 300.

Ta ci gaba da cewa duk wadanda suka ci gajiyar shirin za su rika samun sakonnin taya murna da na wayar da kai a cikin kwanaki masu zuwa, domin sanar da su cewa an zabe su.

A cewar Sadiya Umar-Farouq, kudaden da ake baiwa wadanda suka ci gajiyar shirin bashi ne ba kyauta ba kuma dole ne a biya su cikin watanni tara.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

16 − eight =