Buhari yace harin NDA ba zai hana kawo karshen ta’addanci ba

62

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya ce harin da ‘yan fashin daji suka kai Kwalejin Horon Sojoji ta NDA, zai sa gwamnatinsa ta hanzarta daukar mataki maimakon sanyaya mata gwiwa.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Femi Adesina ya fitar, Buhari ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan sojoji biyu, da maharan suka kashe ranar Litinin da tsakar dare, inda yace za a bi kadin kisansu.

A cewar sanarwar, ganin cewa harin na zuwa ne a lokacin da sojoji suka matsa wa ‘yan fashi, da masu garkuwa da mutane da sauran masu laifi, shugaban kasa ya ce wannan mummunan aikin zai jawo hanzarta kawo karshen rashin imani kwatakwata, kuma abin da sojoji ke yunkurin cimmawa kenan cikin kanƙanin lokaci.

Sanarwar da aka fitar a yau ta kara da cewa, Shugaba Buhari yace maimakon hakan ya sanyaya gwiwar dakarun sojin kasarnan kamar yadda aka tsara, sai dai ya kara musu azama wajen kawo karshen miyagu a kasarnan.

A wani labarin kuma, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya gana da Gwamna Simon Lalong na jihar Filato ta sirri a fadarshi dake Abuja.

Da yake zantawa da manema labarai na fadar gwamnati a karshen zaman, gwamnan ya ce ya yiwa shugaban kasa bayani dangane da cigaban tsaro a jihar Filato.

Ya ce Shugaba Buhari ya yi alkawarin cewa, za a bayar da tallafi ga wadanda rikicin da ya barke a jihar ya shafa.

Dangane da kisan matafiya da aka yi kwanan nan a Rukuba, kusa da Jos, da sauran rikice-rikicen tashin hankali a jihar, gwamnan ya sha alwashin cewa za a gurfanar da duk wadanda ke da hannu a ciki ba tare da la’akari da asalin su ba.

A cewarsa, yanayin tsaro a jihar ya inganta sosai kuma nan ba da jimawa ba, za a kara sassauta dokar hana fita da aka sanya a yankunan da ke fama da rikici.

Gwamnan ya kuma yi kira da a kwantar da hankula da kame kai, inda ya kara da cewa wadanda ke kira da a dauki fansa ba su nufin alheri ga jihar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

eleven + 18 =