Sojin najeriya za su dauki wasu daga cikin tsaffin sojoji domin yakar rashin tsaro

28

Hukumar Sojin Najeriya tace ta fara daukar wasu daga cikin sojojin da suka yi ritaya aiki domin dakile karuwar rashin tsaro a kasarnan.

Shugaban Sojojin Kasa, Laftanal Janar Attahiru Ibrahim, ya fadi haka a jiya lokacin da yake bude taron karawa juna sani na tsaffin sojoji wanda aka gudanar a Fatakwal ta jihar Rivers.

Attahiru Ibrahim, wanda ya samu wakilcin, Manjo Janar Abdulrasheed Aliyu, yace har yanzu tsaffin sojojin suna da rawar da zasu taka, duk da kasancewar sun yi ritaya daga aiki.

Ya kuma kara da cewa taron karawa juna sanin zai kara sanin makamar aiki ga tsaffin sojojin a bangarorin dabaru da kwarewar da ake bukata domin habaka tsaron kasa.

Janar officer na barikin soji ta 6 dake Fatakwal, Manjo Janar Sani Mohammed, yace an zakulo mahalarta taron daga barikoki daban-daban, da sassa da kauyukan dake kudancin kasarnan.

Gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers ya bayyana kudirin da shugaban sojojin ya fito da shi a matsayin abin a yaba.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

4 + 12 =