Buhari ya nada Usman Baba a matsayin shugaban ‘yansanda

58

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Usman Alkali Baba a matsayin mukaddashin sufeto janar na yansandan kasa.

Ministan harkokin yansanda, Mohammed Maigari Dangyadi, ya sanar da haka a yau lokacin da yake jawabi ga manema labaran fadar shugaban kasa.

Yace nadin na Usman Baba ya fara aiki nan take.

A ranar 4 ga watan Fabrairun bana, Shugaba Buhari ya kara wa’adin mulkin Mohammed Adamu a matsayin Sufeto Janar na yansanda da watanni 3.

Sai dai, Mohammed Adamu, ya shafe wata 2 da kwana 3 daga cikin karin wa’adin da aka yi masa na wata uku, kafin nadin Usman Baba. Nadin mukaddashin sufeto janar na yansanda sai ya samu sahalewar zaman ganawar majalisar kasa, wanda ake shirin kira nan bada dadewa ba.

Kafin nadinsa, Usman Baba, Mataimakin Sufeto Janar na Yansanda ne mai kula da sashen bincike a helkwatar yansanda.

An haife shi a ranar 1 ga watan Maris na shekarar 1963, a garin Geidam na jihar Yobe, Usman Baba ya shiga aikin dansanda a ranar 15 ga watan Maris na shekarar 1988.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

20 − 13 =