Boko Haram sun kone makaranta da asibiti a Katarko, jihar Yobe

149

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne da sanyin safiyar jiya sun kone wani sansanin sojoji, makaranta da kuma cibiyar kiwon lafiya a kauyen Katarko da ke karamar hukumar Gujba a jihar Yobe.

Kauyen Katarko yana da kimanin kilomita 25 gabas da Damaturu, babban birnin jihar.

Asusun tallafawa wadanda rikicin Boko Haram ya shafa ne ya gyara makarantar firamaren da aka kone ‘yan shekarun da suka gabata bayan da mayakan suka kone ta a shekarar 2013.

Rahotannin da ba a tabbatar da su ba sun nuna cewa wata Kungiya mai zaman kanta ta ajiye kayan abinci a makarantar don rarrabawa, amma mayakan suka samu labarin kuma sun yanke shawarar kai hari makarantar tare da kwashe kayan abincin.

Mazauna kauyen sun ce ‘yan bindigar sun kuma mamaye cibiyar kula da lafiya matakin farko a kauyen tare da cinnawa wurin wuta bayan sun wawushe magunguna.

Wani mazaunin garin, Modu Katarko, ya shaidawa manema labarai cewa maharan sun zo da misalin karfe 5:30 na safiyar jiya kuma sun bar kauyen ba tare da fuskantar kalubale ba bayan sun shafe fiye da awa daya.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

twenty − seventeen =