Majalisar Dinkin Duniya tana kaddamar da neman kudi dala biliyan daya, kwatankwacin naira biliyan 381, a Abuja, domin taimakawa mutanen dake bukatar agaji a Arewacin Najeriya sanadiyyar rikice-rikice.
Kungiyar Boko Haram ta na kai hare-hare a yankin tsawon shekara 11.
Sama da mutane dubu 30 ne suka mutu kuma aka raba miliyoyi da muhallansu cikin shekarun.
Majalisar Dinkin Duniya tace kimanin mutane marasa karfi miliyan 9 ne suke bukatar agaji a yankin.
Shirin na agazawa mutane na kokarin taimakawa mutane miliyan 6 da rabi a bana, a yankunan da lamarin yafi kamari a jihoshin Borno da Yobe da Adamawa.
Majalisar dinkin duniya da gwamnatin tarayya sun ce annobar corona ta kara lalata ayyukan tallafawa mutane.