Wasu yan bindiga sun sace dalibai mata fiye da 300 daga makarantar sakandiren yanmata ta Jangebe da ke karamar hukumar Talata-Mafara a jihar Zamfara, jiya Alhamis da daddare.
Mahaifin daya daga cikin daliban da kuma wani malami da ke makarantar lokacin da aka sace daliban sun tabbatar da aukuwar lamarin.
Kazalika wani ganau ya ce an tabbatar da sace mata fiye da 300 ne sakamakon kirga dukkan ‘yan makarantar da suka rage bayan barayin sun sace daliban.
Haka kuma wani mutum da aka sace ‘yarsa daya mai suna Bilkisu da ‘ya’yan ‘yan uwansa biyu, ya ce daruruwan ‘yan bindiga ne suka isa makarantar inda suka soma da kai hari kan masu gadi kafin su yi awon gaba da daliban.
Da yake tabbatar da lamarin ga manema labarai, kakakin yansanda na jihar, Mohammed Shehu, yace sun fara bincike.
Wannan na zuwa ne yayin da ake kokarin kubutar da daliban makarantar sakandiren Kagara da malamansu da yan bindiga suka sace a jihar Neja.