A yanzu dai, ana kusan kan-kan-kan a zaben shugaban kasar Amurka tsakanin Donald Trump da Joe Biden inda Biden din ya tsere wa Trump da kuri’u kadan.
Masu goyon bayan Joe Biden na jam’iyyar Democrat dai na ikirarin alamu sun fara nuna cewa sakamakon zaben da ke fitowa na nuni da alamun nasara a garesu.
Sai dai Trump na Jam’iyyar Republican, ya yi ikirarin lashe zaben kuma ya sha alwashin kai kara Kotun Koli domin kalubalantar zaben.
A yanzu dai akwai miliyoyin kuri’u wadanda ba a kidaya ba, kuma babu wani dan takara da zai iya ikirarin lashe zaben.
Kasar ta Amurka tana daf da samun mafiya yawan mutanen da suka fito zabe a cikin shekaru 100. Sama da mutane miliyan 100 ne suka kada kuri’a a zaben wuri kafin ranar zabe, kuma gommman miliyoyin mutane sun yi nasu zaben a jiya.
A halin da ake ciki a kasar, akwai yiwuwar baza a samu cikkaken sakamakon zaben ba sai nan da kwanaki.