Rundunar yansandan jihar Kaduna ta kame akalla mutane 25 da take zargi da wawashe kayayyaki mallakin gwamnati da yan kasuwa, kasancewar wasu bata gari sun kwace zanga-zangar EndSARS.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, Mohammed Jalige, ya sanar da haka a wajen taron manema labarai a Kaduna.
Yace biyo bayan halin da ake ciki dangane da zanga-zangar EndSARS a kasarnan da yadda bata gari suka kwace zanga-zangar daga baya, an samu matsalar kwashe kaya da lalata kadarori a jihar.
Yace a sanadiyyar hakan, gwamnatin jihar ta kakaba dokar hana fita gabadaya ta awanni 24, domin dakile ayyukan bata gari da yan daba.
Mohammed Jalige yace kasancewar hakkin yansanda ne da sauran hukumomin tsaro tabbatar da bin doka, hukumar yansanda ta bazama bakin aiki.