Sojoji sun kama mutane 158 da ake zargin mahara ne a Katsina da Zamfara

78

Hukumar Sojin Najeriya tace dakarun shirin Operation Sahel Sanity sun kama wasu mutane 158 da ake zargin barayi ne a ayyukan kakkabe barayin a jihoshin Katsina da Zamfara.

Mukaddashin daraktan yada labarai na Operation Sahel Sanity, Bernard Onyeuko, ya sanar da haka yayin taron manema labarai a sansanin soji na musamman dake Faskari a jihar Katsina.

Onyeuku ya sanar da cewa dakarun wadanda suka yi aiki da bayanan sirrin da suka samu, sun fatattaki wani wajen hakar ma’adanai ta barauniyar hanya a yankin karamar hukumar Bukkuyum dake jihar Zamfara, inda suka kama barayi 150 tare da kwace bindigogi 120.

Yace dakarun sun kama mamayi wani sansanin barayin a yankin karamar hukumar Anka ta jihar Zamfara, inda suka kashe wani barawo daya tare da kama wasu biyu, kuma suka kwace bindiga samfurin AK47 guda biyu, da kwanson harsasai biyu tare da babura.

Yayi nuni da cewa an mika mutanen da ake zargin barayine ga rundunar yansandan jihar Zamfara domin cigaba da bincike.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

five × 5 =