Saudiyya ta sanar da cewa za a gudanar da Hajji da mutane ‘yan kalilan a bana sanadiyyar annobar coronavirus, inda mutane dake zaune a kasarne kadai za a bawa damar shiga aikin hajjin wanda za a fara a karshen watan Yuli mai zuwa.
Shawarar hakan tazo ne bisa la’akari da karuwar masu kamuwa da cutar corona a fadin duniya, da rashin rigakafi da kuma wahalar tabbatar da bayar da tazara tsakanin dumbin mutanen da zasu so aikin hajjin daga kasashen waje.
Sama da mutane miliyan 2 ne suke gudanar da hajji kowace shekara a kasar, dayawa daga cikinsu suna zuwa daga kasashen waje.
Aikin Hajjin zai zama barazana wajen yaduwar cutar, kasancewar miliyoyin alhazai na cunkusuwa a guraren ibada dake cika makil.
Karamin aikin Hajjin da za a yi ya bayyana asarar makuden kudaden shiga ga kasar, wacce tuni take fama da koma bayan da dokar takaita zirga-zirga da faduwar farashin danyen mai suka haifar.