Jirgin Kasa A Indiya Ya Take Ma’aikata ‘Yan Gudun Hijira Inda Ya Kashe 14

155

Wani jirgin kasa a Indiya ya bi ta kan wasu ma’aikata ‘yan gudun hijira lokacin da suke barci akan digar jirgi yau Juma’a, inda ya kashe akalla 14 daga cikinsu, wadanda ga dukkan alamu suna kan hanyarsu ta komawa kauyukansu, a cewar ma’aikatar jiragen kasa da kafafen yada labarai.

Gomman dubban mutane ne ke tafiya a kafa zuwa gida daga manyan biranen Indiya, bayan sun rasa ayyukansu sanadiyyar dokar kulle domin dakile bazuwar cutar corona tun bayan karshen watan Maris.

Direban jirgin yayi kokarin tsayar da jirgin kasan lokacin da ya hangi leburorin kwance akan diga a jihar yammaci ta Maharashta, a cewar ma’aikatar jiragen kasa, inda ta kara da cewa ta bayar da umarnin gudanar da bincike.

Karkashin dokar kullen, an dakatar da dukkan zirga-zirgan motocin haya, sabili da haka, ma’aikata ‘yan gudun hijira wasu lokutan su kanyi tafiya mai nisa a kasa domin isa inda suka nufa.

Gwamnati ta kara wa’adin dokar kullen har zuwa ranar 17 ga watan Mayu.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

6 + 14 =