![soldiers](https://skydaily.ng/hausa/wp-content/uploads/2025/02/soldiers.webp)
Rundunar Fansan yamma da ke yaƙi da ƴan bindiga a jihohin Zamfara da Sokoto ta ce ta samu gagarumar nasarar karya lagon “yanta’adda” daga ranar 1 zuwa 10 ga watan Fabrairun 2025.
Rundunar wadda ta shaida hakan a wata sanarwa da ta fitar ta hannun mai magana da yawunta, Laftanar Kanar Abubakar Abdullahi, ta ce aikin da rundunar ta yi ya ci galaba kan “ƴanta’adda” da suka haɗa da manyan ƴanbindiga.
A yayin aikin rundunar, dakarun soji sun yi nasarar kashe gomman “ƴanta’adda” da suka haɗa da manyansu irin su Kachalla na Faransa da Dogon Bakkwalo da Auta Gobaje da Dan Mai Dutsi.
Sanarwar ta ce yawancin ƴanbindigar na addabar al’ummar yankunan da ke ƙananan hukumomin Shinkafi da Zurmi da ke jihar Zamfara da kuma ƙaramar hukumar Isa ta jihar Sokoto
BBC Hausa