
Daga Ibrahim Imam Ikara
Kasancewar Malam Nuhu Ribadu a matsayin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, haƙiƙa ya dawo da martabar tsaron Najeriya, domin an miƙa ragamar tsaron a hannun jajirtaccen namiji ɗan kishin ƙasa, mai gaskiya da amana, wanda ke da ƙwarewa a aikin ɗan sanda da kuma bincike.
Malam Nuhu Ribadu ya na amfani da ƙwarewa da basira wurin murƙushe ta’addanci a Najeriya, musamman wasu jihohin Arewa in da matsalar tsaron ta fi yawa.
Malam Nuhu Ribadu ya yi ƙoƙarin kawar da siyasa a yaƙi da ta’addanci, ta yadda yake aiki tuƙuru ba ta hanyar yin amfani da ƙarfi ba kawai, har ƙofar tuba da afuwa tare da tuntuɓa an buɗe, domin tsayar da zubar da jini da kuma inganta tsaron Najeriya.
Kuma tabbas kwalliya na biyan kuɗin sabulu, domin mun ga yadda wannan salon na yin sulhu ya yi aiki a jihar Kaduna, kuma mun ga yadda wancan salon ya yi aiki ta hanyar kawar da manyan ƴan bindiga da suka addabi al’umma kamar irin su Halilu Sububu.
Wani abin ban sha’awa ga Malam Nuhu Ribadu shi ne yadda yake aiki cike da kishin ƙasa, ta yadda ya haɗa kai da dukkan jami’an tsaro da sauran shugabanni domin inganta tsaron Najeriya.