Daga Adamu Inuwa Lawan
Tunda rikicin Isra’ila da Yankin Zirin Gaza ya ɓarke a Gabas ta Tsakiya, ranar bakwai ga watan Oktoba na shekarar 2023, duniya ta yi Allah wadai da salon yaƙin da kuma muhimmin goyon baya kamar su tallafin kuɗi, makaman yaƙi, da bayanan sirri da ƙasar Amurka ke ba wa ƙasar Isra’ila. Wannan yaƙi ba ƙaramin sarƙaƙiya ba ne dashi domin a yanzu haka, ƙasar Amurka tana ta ƙoƙarin haɗa kan ƙasashe da ƙungiyoyi masu faɗa aji a wannan yanki don kawo ƙarshen rikicin. Sai dai babban ƙalubale da ake fuskanta yanzu shi ne, Firaminista Bibi Netanyahu ya nuna aniyar dulmiyar da yankin gaba ɗaya cikin mummunan rikici.
Netanyahu ya fahimci cewa rashin wannan rikici zai zama babban kalubale ga makomar siyasar sa a ƙasar. Da zarar an ce yaƙi ya ƙare, za a gudanar da zaɓe a ƙasar Isra’ila, wanda zai iya haifar da rasa kujerarsa ta Firaminista. Amma idan yaƙin ya ci gaba, zai ci gaba da riƙe madafan ikon ƙasar, domin cika burinsa na zama Mahadi, wanda shi kaɗai zai iya kare Isra’ila daga abokan hamayyarta na yankin. Wannan shiri nasa ya zama bayyananne lokacin da ya umurci kai harin da ya kashe manyan jami’an sojojin ƙasar Iran na IRGC a ofishin jakadancin ƙasar dake Siriya, abin da ya kusa haddasa mummunan yaƙi tsakanin Isra’ila da Iran.
Wannan harin, da kuma kashe Shugaban Siyasar Falasɗinawa, Isma’il Haniyeh, a Iran, ya tabbatar da cewa Netanyahu ba shi da niyyar haɗa kai don samun zaman lafiya a yankin tun bakwai ga watan Oktoban 2023. Yaƙin nan, a zahiri, ya koma wani tsari na neman ƙara gindin zama akan karagar mulki, wanda yake tabbatar da tsoron Netanyahu ya sauka daga kujerarsa don kar ya fuskanci tuhume-tuhumen cin hanci da rashawa da ke gabansa a babbar kotun ƙasar.
Saboda haka, wannan yaƙi ya zama fiye da batun tsaro kawai, yana tattare da manyan abubuwan da suka shafi siyasa da kuma makomar Netanyahu a matsayin Firaminista. Idan ba a yi hoɓɓasa daga ƙasar Amurka da sauran ƙasashen duniya ba, za a ci gaba da samun rikicin da zai dagula zaman lafiya a yankin. Yanzu yadda komai ya ƙara cakuda, ƙasashen da suke tattauna batun ya kamata su miƙe tsaye don samun mafita.
A lokaci guda, Amurka ya kamata ta fahimci cewa ba duk Yahudawan Isra’ila ko mazauna wasu birane a faɗin duniya ba ne suke goyon bayan wannan yaƙi. Da dama sun fahimci cewa wannan yaƙi ba komai ba ne face ƙoƙarin Netanyahu na tsira daga ƙalubalen siyasa. Idan Amurka ta buɗe idanunta, za ta ga cewa hanyar zaman lafiya tana buƙatar fahimtar manyan abubuwan da ke haifar da wannan rikici, da kuma sauya dabarun da suka fi mayar da hankali kan kare muradun siyasa na mutum ɗaya kawai.
Allah ya kawo mana zaman lafiya a duniya baki ɗaya.
Lawan ya rubuto wannan ra’ayin nasa ne daga Nguru, Jihar Yobe