wata Kotun daukaka kara dake zaman ta a Abuja ta yi watsi da yunkurin gwamnatin tarayya na sake gurfanar da tsohon gwamnan Jihar Abia Orji Uzor Kalu kan badakalar da alhumdahanar kudi Naira Bilyan 7.6.
A hukuncin da ya gabatar,Mai shari’a Joseph Oyewole yace rahotannin da gwamnatin tarayya ta gabatar basu da sahihancin da kotu zata yi amfani su .
Mai shari’a Oyewole yace bayanan da gwamnatin tarayya ta gabatar sun sabawa dokokin shari’a.
A watan Disembar shekarar 2019 wata babbar kotun tarayya ta bada umarnin daure tsohon gwamnan a gidan wanda yanzu shine Sanatan dake wakiltar Arewacin Jihar Abia,bisa zargin satar kudin Jihar a lokacin da yake gwamna.