SOJOJIN NAJERIYA SUN HALAKA WANI KASURGUMIN DAN BINDIGA A JIHAR KATSINA

4

Sojojin Najeriya sun hallaka jagoran ‘Yan ta’adda mai suna Mai Kusa wanda shine shugaba na 2 a kwamandojin ‘Yan bindiga da masu garkuwa da mutane da suka addabi Jihar Katsina karkashin jagorancin daya daga cikin jagororin ‘Yan bindigar mai suna Modi-Modi.

Bayanin haka na kunshe ne cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai na sojin kasa Manjo Janar Onyema Nwachukwu ya fitar.

A cewar sanarwa,sojojin sun samu nasarar harbe Mai Kusa tare da wasu ‘Yan ta’adda guda 3 a wani gumurzu tsakanin dakarun da kuma ‘Yan ta’addar da ya wakana a kananan hukumomin Kurfi da Safana na Jihar.

Sanarwar ta kara da cewa a lokacin gumurzun,sojojin sun yi nasarar murkushe ‘Yan ta’addar wanda suka addabi yankunan yayinda wasu daga cikin su suka tsere.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

9 − three =