MATAR SHUGABAN KASA TA YI KIRA A SAMAR DA DOKAR KISA KAN MASU GARKUWA DA MUTANE

57

Matar shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta yi kira ga gwamnonin jihohi da ‘Yan majalisun dokoki su samar da dokar kisa kan masu garkuwa da mutane.

Yayinda take nuna takaici dangane da sace dalibai da wasu mata ‘Yan gudun hijira, Remi Tinubu, ta bayyana lamarin a matsayin rashin tausayi matuka.

Hadimin matar shugaban kasa a kafafan yada labarai Busola Kukoyi, ya Ambato Remi Tinubu, ta fadi haka ne a wurin taron shugabannin mata na jami’iyyar APC wanda ya gudana a fadar shugaban kasa.

Sanata Remi,ta fadawa matan cewa shirin kyakkawan fata na gwamnatin shugaba Tinubu zai samar da damarmaki ga mata domin su bunkasa tattalin arziki su, zamantakewa da kuma fannin siyasa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

three × 5 =