MAKARANTU A JIHOHI 14 NA NAJERIYA NA CIKIN BARAZANAR FUSKANTARI DAGA ‘YAN TA’ADDA

4

Gwamnatin tarayya tace wasu makarantu a jihohi 14 na kasar nan ciki hadda babban birnin tarayya Abuja na cikin barazanar farmaki daga ‘Yan bindiga ko ‘Yan ta’adda, yayinda ake samun karuwar yawaitar sace dalibai.

Shugabar shirin samar da kuɗaɗen bayar da kariya ga makarantu na ƙasa Hajiya Halima Iliya, ta ce hukumar ta tattara bayanai da za su taimaka wajen kai wa makarantun ɗauki.

A shekarar 2014 ne aka kafa hukumar bayan sace ɗaruruwan ɗaliban makarantar Chibok da ke jihar Borno a arewa-maso-gabashin ƙasar.

A cewar hukumar Jihohin da wasu makarantunsu ke cikin haɗarin sun haɗa da Adamawa, Bauchi, Borno, Benue, Yobe, Katsina, Kebbi, Sokoto, Filato, Zamfara da birinin Abuja.

A ranar Alhamis da ya wuce ne ƴanbindiga suka sace ɗalibai 270 na makarantun firamare da sakandire a ƙauyen Kuriga da ke jihar Kaduna.

Haka kuma a ranar Asabar da ta wuce ne wasu ƴanbindigar suka sace ɗaliban makarantar tsangaya kimanin 15 a ƙaramar hukumar Gada a jihar Sokoto.

Sace-sacen sun biyo bayan sace wasu ɗaruruwan ƴangudun hijira a Ngala da ke jihar Borno da ake zargin ƴanBoko Haram da aikatawa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

2 × two =