
Kakakin majalisar wakilai Tajuddeen Abbas,ya yi Allah wadai da sace daruruwan ‘Yan gudun hijira a Jihar Borno da wasu dalibai a Jihohin Kaduna da Sokoto.
Yayi kira ga hukumomin tsaro da su bi duk inda ‘Yan ta’addan da suka yi garkuwa da mutanen a Jihohin uku domin kubutar da wadanda harin ya rutsa da su.
Tajuddeen Abbas yayi wannan kira ne cikin wata sanarwa da hadimin sa a kafafan yada labarai Musa Abdullahi Krishi, dangane da sace dalibai a wata tsangaya dake Jihar Sokoto.
Ya kuma yi Allah wadai da ‘Yan gudun hijira da wasu dalibai a Jihar Kaduna.
Idan za’a iya tunawa ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da dalibai 15 a makarantar Islamiyyan Gidan Bakuso a karamar hukumar Gada a jihar Sokoto.
Kakakin majalisar ya bukaci sojoji da hukumomin tsaro su bi sahun masu garkuwa da mutanen don kubutar da wadanda aka sace.
