Majalisar dattawa ta ce zata gana da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu dangane da matsalolin tsaro a Jihar Benue dama kasa baki daya.
Wannan ya biyo bayan mutuwar mutane 30 biyo bayan arangama da kungiyoyi masu dauke da makamai a Jihar Benue.
Matakin na majalisar dattawa ya biyo bayan wani kudiri da aka gabatar yayin zaman majalisar, dangane da kashe-kashe da fadan makiyaya da tsanantar matsalolin tsaro a yankin kwande, Ukum, Logo da karamar hukumar Katsinan-Ala ta Jihar Benue.
Sanata Emmanuel Udende dake wakiltar mazabar Benue Arewa maso gabas shine ya gabatar da wannan kudirin.