Majalisar dattawa ta yi kakkausar suka kan Sanata Abdul Abdul Ningi bisa zargin yin cushe a kasafin kudin shekarar 2024.
A wani zama da suka yi mai cike da hayaniya, wanda aka haska a gidan talabijin na Channels,wasu fusatattu a majalisar dattawan sun dakatar da shi na tsawon watanni uku ta hanyar jin ra’ayin jama’a.
Kazalika,an gargadi Sanata Kawu Sumaila da ya dena yada labaran karya da su iya tada zaune tsaye a majalisar.
Dakatarwar da aka yiwa Abdul Ningi da gargadin da aka yiwa Kawu sumaila ya biyo bayan amincewa wani kudiri da aka gabatar yayin zaman majalisar.
Kudirin da shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar Solomon Adeola, ya gabatar ya samu goyan bayan Sanata Joel Onowakpo Thomas.
A wata hira da sasashen Hausa na BBC Sanata Ningi yayi zargin cewa an yi cushen Naira Tiriliyan 3.7 a kasafin kudin shekarar 2024, lamarin da ya baiwa galibin ‘Yan majalisar mamaki.
Sai dai shigaban kwamitin kasafin kudi na majalisar dattawan Sanata Solomon Adeola, yace wannan zargi baida tushe balanta makama.