MA’AIKATAR ILIMI A NAJERIYA TAYI KIRA DA CETO DALIBAN DA ‘YAN BINDIGA SUKA SACE A JIHAR KADUNA

5

Ma’aikatar Ilimi ta kasa ta yi kira da a gaggauta ceto daliban makarantar Firamare da aka sace a Jihar Kaduna domin sada su da iyalan su.

Akalla daliban makaranta sama da 300 ‘Yan bindiga suka sace a Jihar Kaduna a farkon makon da ya gabata.

Da yake jawabi ga manema labarai a Jiya, Ministan ilimi Tahir Mamman ya bayyana sace daliban a matsayin abun takaici.

Ma’aikatar Ilimin ta bukaci hukumomin tsaro da gwamnatin Jihar Kaduna su yi duk mai iyuwa a ceto daliban da malamin su guda domin sada su da iyalan su.

Ministan ilimi Tahir Mamman,ya jadadda bukatar daukar matakin gaggawa, inda yayi kira ga wadanda ke da alhakin ceton yaran su ninka kokarin su domin kubutar da su.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

thirteen − twelve =