GWAMNATIN TARAYYA TA YI ALKAWARIN HADA GWIWA DA HUKUMAR NDLEA WAJEN KAFA KUNGIYOYIN YAKI DA MIYAGUN KWAYOYI A MAKARANTUN SAKANDIREN JIHAR KWARA

11

Gwamnatin jihar Kwara ta yi alkawarin hada gwiwa da hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa wajen kafa kungiyoyin yaki da shan miyagun kwayoyi a dukkan makarantun sakandire na Jihar.

Hakan na nufin wayar da kan dalibai illar ta’ammali da miyagun kwayoyi a cikin al’umma.

Mai taimakawa gwamnan kan harkokin yaki da miyagun kwayoyi Mukail Aileru,shine ya bayyana haka yayin da daliban sakandiran gwamnatin Jihar Ilorin suka shirya wani shiri da zai taimaka wajen magance ta’ammali da miggan kwayoyi a makarantun Jihar.

Da yake jawabi yayin taron,kwamandan hukumar NDLEA a Jihar Ibrahim Mohammed,ya koka dangane da yaduwar shan miyagun kwayoyi a Jihar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

eleven − 8 =