GWAMNATIN TARAYYA TA KAMA MOTOCIN DAKON KAYA 141 MAKARE DA BUHUNAN HATSI DA SAURAN KAYAYYAKI DA AKA YI YUNKURIN SUMOGAR SU

10

A cigaba da daukar matakan magance matsalar hauhawar farashin kayayyaki da kuma tsadar rayuwa, gwamnatin tarayya tace kawo yanzu ta kama manyan motocin dakon kaya 141 makare da buhunan hatsi da sauran kayayyaki da aka yi yunkurin sumogar su.

Babban kwanturolan hukkumar hana fasa kwari ta kasa, Bashir Adeniyi, yace cikin makonni biyu jami’an hukumar sun kama manyan motocin Tirela kimanin guda 120 dauke da kayayyakin abinci da zummar yin sumagar su daga gida Najeriya, yayinda a nata bangaran hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta hana wasu motocin tirela guda 21 makare da kayan abincin ficewa zuwa kasashe waje.

Yayin da babban kwanturolan ke bayyana irin matakan da hukumar ta dauka na tabbatar da samar da abinci a zauren majalisar wakilai ta kasa,a waje daya kuma direbobin manyan motocin da ‘yan ta’adda suka kaiwa farmaki sun yi barazanar shiga yajin aiki,muddin lamarin ya cigaba da faruwa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

2 × two =