
Gwamnatin Najeriya tace, ta gayyaci sanannen Malamin addinin Islaman nan mazaunin Jihar Kaduna domin yayi karin bayani dangane da wasu kalaman sa kan ayyukan ‘yan bindiga a kasar.
Ministan yada labaran Najeriya Muhammad Idris, ne ya bayyana haka yayinda yake yiwa manema labarai na fadar shugaban kasar karin bayani.
Muhammad Idris, yace Sheikh Gumi, bai fi karfin doka ba.
Yace don haka ya zama wajibi gwamnati ta gayyace shi domin ya amsa tambayoyi dangane da kalaman sa na ayyukan ‘yan bindiga a Najeriya.
