
Babban bankin kasa CBN ya karfafa matakan sanya ido domin gano laifukan da ake aikatawa a bankuna da kuma tabbatar da bin ka’idoji da dokokin aiki.
A ‘yan kwanankin nan bankuna na shan suka bisa zargin su da hannu a laifukan almundahana.
Hukumar yaki da masu yiwa arzikin kasa zagon kasa EFCC,ta yi kiyasin bankunan kasuwanci nada hannu a laifukan almundahana da kusan kashi 70.
