Kwajelin fasaha ta gwamnatin tarayya a Daura zata fara aiki a kakar karatu ta bana

28

Sakataren Zartarwa na hukumar kula da makarantun kimiyya, Dr. Mas’ud Kazaure, yace sabuwar kwajelin fasaha ta gwamnatin tarayya a Daura zata fara aiki a kakar karatu ta bana, ta shekarar 2019 zuwa 2020.

Dr. Mas’ud Kazaure ya bayyana haka a Daura, yayinda yake gabatarwa Sarkin Daura, Alhaji Farouq Umar, takardar izinin mallakar fili mai fadin kadada 100 wanda gwamnatin jihar Katsina ta bayar domin gina makarantar.

Yace an kammala dukkan shirye-shirye domin fara aiki a makarantar, ciki har da daukar ma’aikatan makarantar na farko.

Daga nan sai yayi kiran neman goyon baya da hadin kai da fahimtar juna daga mutanen da za a gina makarantar a garinsu, domin bayar da dama ga makarantar ta fara aiki kamar yadda ya kamata.

Tunda farko, mai bayar ta shawara ta musamman akan ilimin gaba da sakandire ga Gwamna Aminu Masari na jihar ta Katsina, Dr. Bishir Ruwangodiya, yace gwamnatin jihar ta bayar da sashen karamar sakandire na makarantar sakandiren jeka ka dawo ta Daura, a matsayin kwalejin fasahar ta wucin gadi.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

five + 6 =