Za a aika da sabbin ‘yansanda dubu 10 domin zaben 2023

13

Sufeto Janar na ‘yan sandan kasa, Usman Alkali Baba, a yau ya ce za a tura karin jami’an ‘yansanda dubu 10 domin gudanar da zaben 2023.

Babban Sufeto Janar na ‘yan sandan ya bayyana haka ne a Ilorin, babban birnin jihar Kwara a lokacin da ake gabatar da lacca a wani bangare na taron yaye dalibai karo na 12 na jami’ar Al-Hikmah.

A cewar shugaban ‘yan sandan, neman mika mulki cikin lumana a shekarar 2023 da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi shine babban aikin da ‘yan sandan ke shirin tabbatarwa.

A saboda haka Alkali Baba ya ce za a tura karin jami’an da a halin yanzu suke kammala karatunsu a kwalejojin ‘yan sanda domin kara karfin ‘yan sanda a zaben.

A nasa jawabin, mataimakin shugaban jami’ar Al-Hikmah, Farfesa Nuhu Yusuf, ya ce barazanar tashe-tashen hankula na kara bayyana a kullum, musamman ganin cewa an kada gangar zabe.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

5 × 5 =