‘Yansanda sun tabbatar da garkuwa da mutane biyu a Jigawa

81

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa a jiya ta tabbatar da yin garkuwa da wasu mutane biyu biyo bayan wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai a yankin Andaza dake karamar hukumar Kiyawa a jihar.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Emmanuel Effiom Ekot, ya ce ‘yan bindigar sun kuma harbe wasu mazauna garin su biyu a lamarin da ya faru da yammacin ranar Litinin.

Mazauna yankin sun ce masu garkuwa da mutane dauke da makamai, sun je gidan wanda suka nufa kai tsaye, wanda likita ne mai suna Husseini Yakubu, inda suka yi awon gaba da mahaifiyarsa da diyarsa.

Ya bayyana sunayen wadanda harin ya rutsa da su da Khadija Yakubu mai shekaru 50 da Aisha Shehu mai shekaru 15.

Effiom Ekot ya ce an harbe wani mai suna Musa Dahiru da Sani Nuhu a kafafuwa da hannaye, kuma an kai su asibitin garin.

Ya ce a lokacin da aka aika da jami’an ‘yan sanda zuwa wurin, sun bi sawun ‘yan bindigar zuwa daji inda suka gano cewa masu garkuwar sun zo ne akan babura inda suka gudu da wadanda abin ya shafa. Ya kara da cewa ana kokarin ceto wadanda lamarin ya shafa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

four × two =