Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo ya ce dole ne kasashen Afirka su kauracewa dabi’ar rokon kasashen yammacin duniya domin samun mutunci da kima a idon duniya tare da sauya mummunan ra’ayi game da nahiyar.
Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a yayin bude taron shugabannin kasashen Amurka da Afirka a birnin Washington DC na kasar Amurka.
Nana Akufo-Addo ya bukaci hadin kai a tsakanin ‘yan Afirka domin magance manufa guda da aka sanya a gaba.
Shugaban kasar ya ce nahiyar na da kwarewa da ma’aikata amma tana bukatar hadin kan siyasa domin ganin Afirka ta hau turba.
Kalaman Nana Akufo-Addo sun zo ne a ranar da asusun lamuni na duniya IMF ya amince da baiwa Ghana rancen dala miliyan dubu 3 domin rage koma bayan tattalin arziki da ba a taba gani ba a tarihin kasar.
Shugabannin kasashen Afirka da dama sun hallara a birnin Washington DC domin tattaunawa da gwamnatin Amurka dangane da karuwar tasirin kasashen China da Rasha a nahiyar.