Gwamnan Babban Bankin Kasa, CBN, Godwin Emefiele, ya tabbatar da cewa babu gudu babu ja da baya akan batun aiwatar da shirin kayyade kudaden da za ake fitarwa a bankuna.
Yayi magana akan batun a jiya yayin da yake amsa tambayoyi daga manema labaran fadar shugaban kasa bayan ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari akan abubuwan dake faruwa a CBN da tattalin arzikin a garin Daura na jihar Katsina.
Godwin Emefiele ya kuma sanar da cewa babban bankin na CBN da sauran bankunan kasuwanci sun tattara sama da naira tiriliyan 1 daga cikin takardun kudi na sama da naira tiriliyan 2 da miliyan dubu 700 dake zagayawa a hannun mutane a wajen bankuna.
Yace sabbin takardun kudin da aka buga sun isa bankuna kuma ana aikawa da su zuwa sauran sassan bankunan a fadin kasarnan.
Godwin Emefiele yace kowace kauye a kasarnan na da hanyar hada-hadar kudade, a saboda haka shirin ba zai cutar da su ba.
Yace akwai isassun hanyoyin biyan kudade a Najeriya wadanda za su taimakawa kudirin kayyade kudade wanda aka fara a 2012.