
Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutane bakwai tare da yin garkuwa da wasu biyar a wasu hare-hare da suka kai wasu kauyuka a kananan hukumomin Goronyo da Sabon Birni a jihar Sokoto.
Kauyukan da aka kai harin sun hada da Bare, Kagara, Kojiyo a karamar hukumar Goronyo da kuma kauyen Faji a karamar hukumar Sabon Birni. An bayyana cewa an kashe mutum shida a Bare daya kuma a Kagara.
An kuma bayyana cewa ‘yan bindigar sun kutsa cikin shaguna tare da kwashe wasu kayayyaki daban-daban.
Shugaban karamar hukumar Goronyo, Abdulwahab Goronyo, ya tabbatar da harin, inda ya ce ‘yan bindigar sun kuma yi awon gaba da wasu dabbobi a kauyukan.
A kauyen Faji, an ce barayin sun yi garkuwa da mutane biyar da suka hada da mutum daya da matansa biyu.
Da aka tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Sakkwato, Sanusi Abubakar, ya ce ba a yi masa bayanin hare-haren ba.