Za a fara aikin neman man fetur a Jigawa a mulkin Tinubu – Badaru

80

Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar ya ce za a fara aikin nemo danyen man fetur a jihar a lokacin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.

Gwamnan ya bayyana haka ne da yammacin jiya a lokacin da yake jawabi ga magoya bayan jam’iyyar APC bayan gabatar da tutoci ga ‘yan takarar jam’iyyar a yankin Jigawa ta Arewa maso Yamma.

Ya bayyana haka ne a lokacin da yake mayar da martani game da fara hakar mai a tsakanin jihohin Bauchi da Gombe.

Sawaba ta ruwaito cewa a ranar Talata ne shugaban kasa Muhammad Buhari ya kaddamar da aikin hako mai a jihohin biyu.

Akwai sama da ganga miliyan dubu daya na arzikin danyen mai da iskar gas mai fadin kafa miliyan dubu 500 a Filin Mai da Gas na Kogin Kolmani.

A cewar Gwamna Badaru Abubakar, jihar Jigawa ma tana da arzikin man fetur da za a hako a lokacin gwamnatin Bola Tinubu.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

7 + sixteen =